RUNDUNAR ‘YAN SANDA TA JIHIA KANO NA SANAR DA AL’UMMA CEWA A YAU TALATA NE JAMI’ANTA KE ATISAYEN HARBIN BINDIGA A KEBANTACCEN WURI

Comments are closed

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano na sanar da al’uma cewa a yau Talata ne jami’anta ke atisayen harbin bindiga a kebantaccen wuri dake Hawan Kalibawa na yankin karamar Hukumar Dawakin Tofa a nan jihar Kano.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Magaji Musa Majiya ya sanyawa hannu, ta ce rundunar an fara wannan atisayen harbin ne da misalin karfe 6 na safe zuwa karfe 4 na yammacin wannan rana ta talata.
A don haka rundunar ke shawartar mazauna yankin musamman ma wadanda ke Kauyukan Danbazau da Gangaren Dutse da Tumfafi da Kakurum da kuma Dandalama a yankunan kananan hukumomin Dawakin Tofa da Ungoggo kada su razana.
Sanarwar tace mazauna wadannan yankuna da makwaftan su zasu rinka jin amon bindiga har zuwa karshen lokacin da za’a kammala wannan atisaye.

Comments are closed.