SHUGABANNIN MAJALISAR DOKOKI TA KASA ZA SU YI WANI ZAMAN GAGGAWA A YAU TALATA

Comments are closed

Rahotanni daga Abuja na cewa sugabannin Majalisar Dokoki ta kasa za su yi wani zaman gaggawa a yau Talata.
Batun gyaran kasafin kudi da ke gaban majalisar na biliyan N242 shine zai mamaye tattaunawar shugabannin.
Tuni gwamnatin tarayya ta ambata cewa, za’ayi amfani da wani banagare na kudaden wajen gudanar da zabukan badi
Shugabannin majalisun, za su gana ne tare da shugabannin hukumar zabe ta INEC
Baya ga wannan batu akwai sauraran batutuwa da shugabannin majalisar dattawa da na wakilai za su gana akai.
A hannu guda kuma jami’an tsaro na hukumar DSS sun mamaye harabar majalisar dokoki ta kasa.
Jibge jami’an tsaron ya sanya ko da ma’aikatan majalisar sun gaza shiga cikin ofisoshin su domin gudanar da ayyukan sun a yau da kullum.
Rahotanni sunce tun da misalin karfe 6 na safiya jami’an tsaron suka mamaye harabar majalisar.
Hakan dai na zuwa a dai dai lokacin da ake rade-radin cewa, akwai yunkurin tsige shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki biyo bayan sauya sheka da ya yi daga APC zuwa PDP.

Comments are closed.