SAMA DA ‘YAN KASAR WAJE DUBU 700 NE DA KE KASAR AMURKA NE SUKA WUCE WA’ADIN DA AKA DIBAR MUSU NA WATANNI 12 A TAKADARDUN BISAR SU

Comments are closed

Hukumar tsaron cikin gida ta Amurka da ake kira Homeland Security, ta ce sama da ‘yan kasar waje dubu 700 da ya kamata su fita daga kasar Amurka ne suka wuce wa’adin da aka dibar musu na watanni 12 a takardun bisar su.
A wata sabuwar kididdigar, wacce ake fitawar a duk shekara, ta nuna yadda bakin da visarsu ta kare, suke zama babban sanadin karuwar mutanen da suke zaune a Amurka ba tare da izini ba.
Daga watan Oktoban 2016 zuwa watan Satumbar 2017, an samu mutum dubu dari-bakwai-da-daya -da-dari-tara, da suka shigo Amurka ta jirgin sama ko na ruwa, wadanda bizarsu ta wuce wa’adinta, adadin da ya haura yawan jama’ar jihar Vermont da Wyoming.
‘Yan kasar Canada ne suka fi kowacce kasa yawan wadanda bizarsu ta kare da suka ki fita daga kasar ta Amurka, sai Mexico dake biye da ita, sai Venezuela, sannan sai Birtaniya yayin da Colombia ke biye da ita, sannan sai Najeriya sai China da Faransa da Spain da kuma Jamus wacce ta cike adadin kasashe goma, da ‘yayansu suka zarce wa’adin bizarsu a Amurka.

Comments are closed.