SHUGABAN MAJALISAR DATTIJAI DA SHUGABAN MAJALISAR WAKILAI TA TARRAYA SUNYI ALAWADAI DA MATAKIN DA HUKUMAR TSARO TA FARIN KAYA TA YI NA MAMAYE HARABAR ZAUREN MAJALISAR

Comments are closed

Shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki tare da shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Yakubu Dogara sun yi Alawadai da matakin da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi na Mamaye harabar zauran majalisar a jiya Talata.
Shuwagabannin biyu sun bayyana wannana matakin a matsayin gurgunta demokradiyar kasar nan a cewar su hakan ya saba doka.
A wata sanarwa mai kunshye da sa hannun su da suka fitar, sun bayyana cewa jami’an tsaron na DSS sun hana ‘yan majalisun shiga tare da ma’aikatan majalisar domin gudanar da aikin su.
Sai dai kuma tun a jiya mujadashin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbanjo ya kori shugaban hukumar tsaro ta farin kaya Lawal Daura wanda rahotanni na nuni da cewa Lawal Daura na hannun jami’an ‘yansanda suna cigaba da tsare shi domin jin hanzarin sa.

Comments are closed.