GWAMNAR JIHAR IMO YA BAYYANA CEWA WASU GWAMNONIN JAM’IYYAR PDP DAGA KUDU MASO GABASHIN KASAR NAN ZASU DAWO JAM’IYYAR APC

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya bayyana cewa nan bada jimawa ba wasu gwamnonin jam’iyar PDP biyu daga kudu maso Gabashin kasar nan zasu dawo jam’iyar APC.
Rochas, na wadannan kalamai ne yayin da yake ganawa da manema labarai jiya Alhamis a birnin Owerri, cewa gwamnonin na jam’iyar PDP wadanda ba sai ya ambata sunan sub a, nan bada jimawa ba zasu sauya shekar tasu zuwa jam’iyar APC.
Ya kuma ce duk wadanda suke ficewa daga jam’iyar su ta APC ba wani abu bane illa kawai don biyan wasu bukatun kan su ne, yasa suke barin jam’iyar ta APC, wanda yace hakan ba zai hana jam’iyar cigabada da gudanar da ayukan ta na hidimtawa al’ummar kasar nan.
Ya kara da cewar, shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne da yake kishin kasar nan wajan ya ciyar da ita gaba kuma, a don haka yace al’ummar kabilar Igbo na goyon bayan sa wajan ganin ya sake maimaitawa a shekarar 2019.

en_USEnglish
en_USEnglish