AN GARGADI MATASA DA SU GUJI TA’AMMALI DA MIYAGUN KWAYOYI, DON SAMUN INGANTACCIYAR AL’UMMA ANAN GABA

Shugaban kwalejin Sa’adatu Rimi Dakta Yahaya Isa Bunkure ya gargadi matasa da su guji ta’ammali da miyagun kwayoyi, don samun ingantacciyar al’umma anan gaba.
Dakta Yahaya Isa Bunkure ya bayyana hakan ne, yayin da yake karbar bakwancin mambobin Jam’iyyar Matan Arewa a ofishin sa, inda ya ce matsalar shaye-shaye kayan maye na da matukar illa sosai a rayuwar matasa.
Dakta Bunkure ya kara da cewar, gwamnatin jihar Kano na iya kokarinta wajen ganin ta dakile matsalar ta shaye-shaye, a don haka ya ke kira ga matasa da su guji shaye-shayen kayan maye duba da sune jagorori anan gaba.
Ya kuma ce, gwamnatin kano na hada kai da dukkanin bangarorin tsaro don magance matsalar ta shaye-shayen a fadin jihar nan, sannan kuma ya bukici iyaye da su rinka kula da kai kawon ‘ya’yan su tare da janyo su a jiki don fadawa halin na shaye-shaye.
Da ta ke jawabi shugabar jam’iyyar ta matan arewa, Hajiya Ummi Tanko Yakasai, ta ce dalilin da yasanya su kai ziyarar, don samun goyon baya daga shugaban kwalejin, wajen cimma muradansu tare da tallafawa mata da kuma matasa wajen wayar masu da kai akan illar shaye-shaye a cikin al’umma, da kuma horas da su sana’oi iri daban-ddaban wadan da zasu amfana a nan gaba.
Ta kuma kara da cewar, daga cikin manufofin su akwai taimakawa mata da matasa a bangaren ilimi, tare da wayar musu da kai acikin dukkannin bangarorin rayuwa.
Hajiya Ummi Tanko yakasai ta kuma bukaci shugabana kwalejin da su hada hannu da hannu wajen bayar da bita akan akan illar shaye-shaye a tsakanin matasa tare da basu gurbin karatu a tsakanin mambobin nasu.

en_USEnglish
en_USEnglish