GWAMNATIN JIHAR KANO TA WARE SAMA DA MILIYAN DARI UKU DA HAMSIN DOMIN TALLAFAR DALIBAI A HARKAR ILIMI

Gwamnatin Jihar Kano ta ware tare da raba sama da Naira Miliyan dari uku da hamsin, don tallafawa dalibai dubu 14 da 477 ‘yan asalin jihar kano, da ke karatu a makarantu daban-daban a fadin kasar nan.
Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hakan ne a ranar litinin din data gabata, yayin kaddamar da taron bada tallafin ga dalibai, wanda ya gudana a kwalejin Sa’adatu Rimi dake nan kano.
Dr abdullahi umar ganduje ya ce bada tallafin wani bangare ne na cika alkawuran da gwamnatotcin baya suka gaza yi, wanda a yanzu gwamnatin wannan lokaci ta aiwatar.
Da yake jawabi shugaban kwalejin Sa’adatu Rimi Dakta Yahaya Isa Bunkure ya bayyana bada tallafin a matsayin wani bangare na cigaban ilimi a jihar kano tare da karfafawa dalibai gwiwa.

en_USEnglish
en_USEnglish