SHUGABAN JAM’IYYAR APC NA JIHAR KANO YA KADDAMAR DA WASU MANYAN KWAMITOCI GUDA BIYU

Shugaban Jam’iyyar APC na nan Jihar Kano Abdullahi Abbas, ya kaddamar da wasu manyan Kwamitoci guda biyu wanda suka hada da Kwamitin Sasantawa da kuma Kwamitin Tuntuba.
Abdullahi Abbas ya bayyana dalilan kafa Kwamitocin da cewa, an samar da su ne domin yiwa wasu daga cikin abubuwan da ake kallo kamar suna da matsala domin kamo bakin zaren.
Ya ce anyi dukkan mai yiwuwa domin zakulo wadannan jajirtattun mutane wadda idan dai kima da mutunci ake bukata to daga kan wadannan mutane sai dai ayi addu’a a tashi, inda yace Jam’iyyar APC da Jam’ar Kano sun gamsu da kyawawan ayyukan da Shugaban Kasa tare da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje keyi.
Kwamitoci guda biyu wanda suka hada da Kwamitin Sasantawa da kuma Kwamitin tuntuba. Yayin da Kwamitin Tuntuba ke karkashin shugabancin Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Kabiru Alasan Rurum a matsayin shugaba, sai kuma mambobin kwamitin da suka hada da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da Sanata Barau Jibril da Hon. Alhassan Ado Doguwa da Abdullahi Tijjani Mohd Gwarzo da Sulaiman Abdurrahaman Kawu Sumaila da Murtala Sule Garo da Musa Iliyasu Kwankwaso da sauransu.
Da yake gabatar da jawabinsa a lokacin kaddamar da kwamitocin guda biyu, Kakakin majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Kabiru Alasan Rurum ya tabbatarwa da shugaban Jam’iyyar cewa zasuyi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da nasarar wadannan Kwamitocin.

en_USEnglish
en_USEnglish