WANI LAUYA YA BAYYANA CEWA TURA YARA ALMAJIRANCI DA IYAYE KEYI YA SABA WA DOKAR KASA

Wani lauya anan kano barrister umar usman danbaito ya bayyana cewa tura yara almajiranci da wasu daga cikin iyaye keyi ya saba da dokar kasa.
Barrister umar usman danbaito ya bayyana hakan ne ta cikin sharia aikace na nan gidan radion dala fm da safiyar yau laraba.
Yace kowanne yaro yana bukatar kulawa ta musamman agun iyayensa da kuma bashi ingantacciyar tarbiya.
Hakazalika gwamnati tana da rawar da zata taka wajen dakile wannan matsala ta tura yara almajiranci,tare da makarantun allo maimakon barin yara suna yawo barkatai a tituna da sunan bara.
Barrister danbaito ya kuma yi kira ga iyaye dasu kula da tarbiyar yayansu domin kaucewa fadawa hanyar da bata dace ba.

en_USEnglish
en_USEnglish