AN JANYE SAMMACEN KAMA SHUGABAN HUKUMAR ZABE MAI ZAMAN KANTA

Kotun Daukaka Kara dake Abuja, ta janye sammacen kama Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Kotun dai karakshin Mai Shari’a Stephen Pam, na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja shine ya bada sammacen a ranar 8 Ga watan Agusta, inda ya umarci babban sfetan ‘yansandan kasa Ibrahim K Idris, da ya kamo shugaban na INEC, sakamakon kin halartar zaman kotun har sau uku.
Game da wani korafi da aka kai gaban kotun jihar Anambra cewa, wani dan siyasa mai suna Ejike Oguebego ya kalubalanci INEC a jihar Anambra, saboda ta ki bayyana shi a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar PDP, kamar yadda Kotun Kolin ta bada umarni cikin watan Disamba, a shekarar 2014.
Rahotanni sun bayyana cewar, kotun daukaka karar ta janye sammacen kama Farfesa Yakubu a jiya Laraba, har sai an karkare da batun daukaka karar da INEC din ta yi.

en_USEnglish
en_USEnglish