GWAMNAN JIHAR PLATO YA CE ZAMAN LAFIYA YA DAWO JIHAR

Gwamnan jihar Plato Simon Lalong ya ce, yanzu haka zaman lafiya ya dawo Jihar, sakamakon matakan da gwamnatin jihar ta dauka tare da taimakon gwamnatin tarayya.
Gwamna Lalong, ya ce yana wurin zaben shugabannin jam’iyyarsa na kasa ya ji labarin kashe kashe ya barke a jiharsa, nan take ya nemi komawa jihar.
tsawon shekaru uku kenan Gwamna Lalong yana mulkin Jihar, amma ba’a samu tashin hankali ba sai wannan shekarar, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin kabilun Berom da Fulani.
Ya ce yanzu sun shirya domin su tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.
Gwamnan yace babu ruwansa da batun addini ko kabilanci saboda ya taso a gidansu inda rabi Musulmi ne rabi kuma Kirista amma duka ‘yanuwan juna ne.
Gwamna Lalong ya ce babu dalilin samar da wasu hanyoyi daban da mutane zasu bi zuwa jihohin arewa maso gabas, maimakon bi ta birnin Jos kamar yadda wasu suka bukaci ayi.

en_USEnglish
en_USEnglish