GWAMNAN JIHAR YA TURA MALAMAN MAKARANTUN FIRAMAREN JIHAR KARO ILIMI

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya tura malaman makarantun firamaren Jihar har su dubu biyar, domin su karo ilimi don samun horo na musamman akan fannin na koyarwa.
Obaseki, ya ce malaman makarantun zasu karo ilimi ne a karkashin hukumar ilimin bai daya ta jihar don ganin an inganta harkar koyo da koyarwa a makarantun firamaren jihar baki daya.
Wannan dai shine karo na biyu da gwamnatin jihar Edo ta tura malaman firamaren karo ilimi tin bayan da aka tura balamai dubu biyu a baya.
Rahotanni na nuni da cewa, gwamnatin jihar ta zabo malaman ne daga cikin makarantun firamaren dake fadin jihar ta Edo sannan kuma a karshe gwamnatin jihar za ta rabawa manyan malaman makarantun wayar hannu.

en_USEnglish
en_USEnglish