GWAMNATIN KENYA TA SOMA TUHUMAR MANYAN JAMI’ANTA DA AKE GANIN SUN FI KARFIN DOKAR KASAR

Gwamnatin kasar Kenya ta soma tuhumar manyan jami’anta da ake ganin sun fi karfin dokar kasar, a wani bangare na kokarin da ta keyi wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
A cikin wannan satin ne gwamnatin kasar Kenya ta tuhumi wasu manyan jami’an ta biyu da suke jin sun fi karfin doka.
Ana dai tuhumar wadannan jami’an ne da laifin cin hanci da rashawa na zunzurutun kudi har dala miliyan 3 na ginin hanyar jirgin kasar da wani kanfanin kasar China ke ginawa a kasar ta Kenya.
Wannan tuhumar na manyan jami’an, wata manuniya ce ga gwamnatin Uhuru Kenyata cewa, ba wani jami’in gwamnati da ya fi karfin doka a yakin da gwamnatin ke yi da cin hanci da rashawa.
Sai dai masu sharhi akan al’amurran yau da kullun suna fata wannan tuhumar za ta kai ga gurfanar dasu har a kai ga yanke musu hukunci, wanda hakan zai zamo abin tarihi da gwamnatin ta Kenyata za ta bari ko kuma yakasance barazana ga ‘yan siyasar kasar.
Rahotanni dai sun ce ana tuhumar babban darektan kanfanin jirgin kasa na kasar Atanas Maina da shugaban hukumar kula da albarkatun kasar Mohammed Swazuri, su ake tuhuma da laifin aringizon dala miliyan biyu na biyan kudin diyya.

en_USEnglish
en_USEnglish