KASAR TURKIYA TA KARA KUDIN HARAJI KAN KAYAN AMURKA DAKE SHIGOWA KASAR

Kasar Turkiya ta kara kudin haraji kan kayan Amurka dake shigowa kasar, a wani matsayi na mayar da martani, kan Amurkan.
A jiya Laraba ne dai Fadar White House ta Amurka, tayi Ala wadai da Karin kudin harajin da kasar Turkiyya tayi wa Amurka akan kayayyakin Amurka da ake shiga dasu cikin kasar.
Wannan dai shine fito na fiton da kasashen biyu kawayen juna dake cikin kungiyar tsaro ta NATO suke yi a tsakanin su.
Yanzu haka dai kasar Turkiyyata ta kara kudin haraji akan kayayyakin Amurka da suka hada da Motocin shiga, da gawayi da dai sauran wasu abubuwa, Karin wanda yakai na dala miliyan 533 kenan.
Turkiyyar tayi hakan a matsayin martini na karin kudin da Shugaba Trump yayi na ninka kudin tama da karafa da kasar ke kaiwa Amurka.
Wannan matakin na Amurka ya samo asali ne bayan da kasar ta Turkiyya tayi na kin sakin wani Ba’Amurke mai suna Andrew Brunson da take tsare dashi akan zargin leken asiri da kuma wasu ayyukan dake da nasaba da ta’adanci.

en_USEnglish
en_USEnglish