KUNGIYAR KWALLON KAFA TA REAL MADRID TA YI RASHIN NASARA A HANNUN ATLETICO MADRID

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun abokiyar hamayyarta ta Atletico Madrid da ci 4 da 2 da suka fafata a was an karshe na cin kofin Super Cup na zakarun nahiyar turai bayan da aka kara lokaci.
Wannan dai shine karo na farko da kungiyar ta fara samun nasara tun bayan da tsohon dan was an gabanta Cristiano Ronaldo ya bar kungiyar tare zuwa kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta kasar Italiya.
Kasar Faransa ta koma ta farko a sabon jaddawalin kasashe da hukumar kwallon kafa ta duniya take fitarwa na wata-wata.
Yayin da kasar Belgium take biye mata a matsayi na biyu sai kasar Brazil a matsayi na uku Crotia a matsayi na hudu kasar Uruguay a mataki na biyar.
Ita kuwa kasar Portugal da Switzerland da Andulisiya da Denmark sune suke bin su a cikin jerin jaddawalin na wannan watan.
Idan kuwa muka dawo nan gida jihar Kano a cigaba da wasan damben gargajiya da ake fafatawa a Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, Shagon Mada ya buge yar Balala, shi kuwa Babba Shasgon Shamsi ya buge Shagon Dogon Auta.
Yayin da Shagon Sarka da Abba Shagon Roget babu kisa, Bahogon Abba ya doke Shagon na Bachirawa, a inda Dada Kwalawa ya buge Dogon Kyallu.
Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, Shagon Guduma da Shagon Kato Babu Kisa, yayin da Shagon Hero ya buge Dunan Yallow, Dan Hausa sun gwabza da Yahya amma babu kisa, a inda Autan Adam ya buge Aljan Horo.

en_USEnglish
en_USEnglish