KWAMISHINAN LAFIYA NA KANO YAYI KIRA GA MA’AIKATAN LAFIYA DA SU RINKA HADA KANSU WANJEN TAFIYAR DA AYYUKANANSU

Kwamishinan lafiya na jihar kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso yayi kira ga ma’aikatan lafiya da su rinka hada kansu wajen tafiyar da ayyuka bai daya ba tare da nuna banbanci atsakanin juna ba.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wani taro da kungiyar Dalibai masu karanta ilimi sanin halayyar Dan adam wato Psychology na jami’ar Yusuf Maitama Sule suka shirya a jiya Laraba.
kwamishinan wanda ya samu wakilcin Dakta Aminu Da’u, ya bayyana cewar, samun daidaito tsakanin kowanne bangare zai bada gudunmawa matuka gaya ga taimakon marasa lafiya.
A nata Jawabin shugabar kungiyar Daliban, Hauwa Ibrahim Khalifa, ta ce makasudin gudanar da taron, domin su wayar da kawunan su wajen gudanar da aiki tare da ma’aikatan lafiya.
Wakilin mu Aminu Abdu baka noma ya rawaito cewar, taron ya samu halartar manyan mutane ciki kuwa har da shugaban karamar hukumar Tarauni, Honarable Habu Zakari P A.

en_USEnglish
en_USEnglish