RUNDUNAR ‘YAN SANDAN ZAMFARA TA SAMU NASARAR CAFKE ‘YAN TA’ADDA TARE DA KWATO BINDIGOGI

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce, ta samu nasarar cafke ‘yan ta’adda 20 tare da kwato wasu bindigogi guda 7 daga maboyarsu a wurare daban daban.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Kenneth Ebrimson ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Gusau, ya kuma ce, sashi na musamman da shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa ta kafa mai suna ‘IGP’s Special Tactical Skuad’ tare da hadin gwiwar jami’an rundunar na jihar suka gudanar da samamen.
Ya ce an kama ‘yan ta’addan ne tare da taimakon bayanan sirri kuma nan bada jimawaba za a gabatar da ‘yan ta’addar ga mane labarai.
Ya kara da cewar, dazarar sun kammala bincike zasu yi holon ‘yan ta’addan da suka kama.
Sannan ya yi kira ga al’umma dasu taimaka da rundunar da bayanai sirri wajen cafke ‘yan ta’addan a duk inda suke a fadin jihar.

en_USEnglish
en_USEnglish