WANI MALAMI A NAN KANO YA BUKACI IYAYE DA SU DAINA YIWA ‘YA’YAN SU AUREN DOLE

Wani malami a nan kano Dakta Naziru Datti Yasayyadi Gwale, ya yi kira ga iyaye da su guji yiwa ‘ya’yan su auren dole a wannan zamani, don samun zaman lafiya mai daurewa a tsakanin ma’aurata.
Dakta Naziru Yasayyadi, ya bayyana hakan ne ta cikin wannan Rayuwa na nan gidan rediyon Dala, inda ya ce ya zama wajibi iyaye da su guji yiwa ‘ya’yan su auren dole har idan suna bukatar zaman lafiya a tsakanin ‘ya’ayn nasu.
Ya ce, auren dole a wannan zamani kan jawo samun sabani a yayin zaman auretayya. Ya kuma kara da cewa, addinin musulunci ya bada dama ga iyaye da su gudanar da bincike yayin auren ‘ya’yan nasu.
Dakta Naziru Datti Yasayyadi, ya kuma ja hankalin iyaye da su rinka yiwa ‘ya’yan su addu’a, don samun al’umma mai albarka.

en_USEnglish
en_USEnglish