WATA KUNGIYA A KASAR KAMARU TACE AN SAMU NASARA A CIGABA DA YAKIN DA AKE YI DA YAN KUNGIYAR BOKO HARAM

Wata Kungiya mai suna Internationnal Crisis Group a kasar Kamaru ta bayyana cewa an samu ci gaba a yakin da hukumomin kasar ke yi da yan kungiyar Boko Haram.
A sabon rahoto da kungiyar ta fitar ta bayyana irin ci gaba da aka samu tare da bukatar Gwamnatin kasar Kamaru ta bulo da wani tsari da zai taimaka domin samarwa tsofin yan kungiyar Boko Haram ayukan yi.
Kungiyar Internationnal Crisis Group dake mayar da hankali zuwa batuntuwan da ya jibanci rikice-rikicen, ta fitar da wasu sabin alkaluma dake nuna irin ci gaba da aka samu a yakin da Kamaru ke yi da yan kungiyar Boko Haram.
Ta ce an samu gaggarumin ci gaba duk da cewa mayakan kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da yi barrazana, tsawon Shekaru biyu an samu mutuwar mutane da dama, kama daga farraren hula da sojoji.
Kungiyar ta buKaci hukumomin kasar Kamaru sun kara zage dantse domin tabbatar da cikkaken tsaro a yankunan arewacin kasar.
Sannan ta kuma bukaci gwamnatin Kamaru da ta bulo da wani shiri da zai taimakawa tsofin mayakan Boko Haram da suka mika kai wajan tallafa masu.

en_USEnglish
en_USEnglish