AYAU NE ZA`A GUDANAR DA JANA`IZAR TSOHON SAKATARE JANAR NA KASAR GHANA

A yau ne za`a gudanar da jana`iza ga tsohon sakatare janar na majalisar dinkin duniya marigayi Kofi Annan, yana da shekaru 80 a watan da ya gabata.
Kwanaki biyu kenan da aka ajiye gawarsa a babban birnin kasar Accra, inda masoya da ‘yan uwa ke zuwa yi masa kallon karshe.
Ana sa ran manyan shugabannin kasashen Afirka za su halarci bikin jana`izar a yau, ciki har da matar marigayi Nelson Mandela wato Grace Mandela,da sabon sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio guterres.
Tun da fari wasu ‘yan kasar Ghana sun yi korafin rashin bude fuskar mamacin, don yin bankwana dashi.kasancewar bisa al`ada ana bude fuskar mamaci don yi masa kallon karshe.

en_USEnglish
en_USEnglish