AN UMARCI BATURAN ‘YANSANDA DA SU FARA AIWATAR DA TARON WAYAR DA KAN AL’UMMA A MATAKIN KANANAN HUKUMOMI

Comments are closed

Rundunar ‘yan sandan Jihar kano ta umarci baturan ‘yansanda wato DPO, da su fara aiwatar da taron wayar da kan al’umma a matakin kananan hukumomi don ganin anyi babban zaben 2019 lafiya.
Kwamishinan ‘yansanda, Rabi’u Yusuf ne ya yi umarnin cikin makon jiya, harma ajiya baturan ‘yansanda na Fagge SP Mansur Idris, ya fara kaddamar da taron a Fagge.
A yayin taron kakakin rundunar ‘yansandan a nan kano, SP Magaji Musa Majiya, ya ce al’ummar Kano suna kokari wajan kiyaye bin doka amma akwai bukatar su daura akan kokarin da suke yi.
Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il, ya rawaito cewa, al’umma da dama ne daga yankin karamar hukumar ta Fagge suka halarci taron.

YNI/ARJ/SDK/TA

Comments are closed.