KUNGIYAR CIGABAN ILIMI DA INGANTA HARKOKIN DEMOKRADIYYA , TA YI KIRA GA AL’UMMA DA SU GUJI CUSA KANSU A CIKIN BANGAR SIYASA

Comments are closed

Kungiyar cigaban Ilimi da inganta harkokin Demokradiyya SEDSAC, ta yi kira ga al’umma musamman matasa, da su guji cusa kansu a cikin bangar siya sa, domin tsira da mutunci su.
wata sanarwa, mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Kwamared Umar Hamisu Kofar Na’isa, ta bayyana cewa, wasu daga cikin ‘yan siyasa na amfani da matasa wajen cimma bukatun su, amma da zarar sun dare kan karagar mulki sai su guji matasan.
Sanarwar ta anbato cewa, Nigeria kasa ce mai arziki a nahiyar afrika, a don haka kamata ya yi matasa suyi amfani da wannan dama wajen inganta rayuwar su.

Comments are closed.