KASASHEN ETHIOPIA DA ERITREA SUN SA HANNU KAN WATA YARJEJENIYA

Kasashen Ethiopia da Eritrea, sun sanya hanu kan wata yarjejeniya da zata kara karfafa dangantaka tsakaninsu, bayan kwashe skeru biyu suna gwabza yaki da kuma sama da shekaru ashirin cikin zaman doya da manja.
Kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a wani taron koli da suka yi a kasar Saudiyya.
Duk da cewa Ba a bayyana sharuddan da suke kunshe cikin yarjejeniyar ba, amma, kasashen sun amince da ita a gaban sarki Salman na saudiyya da babban sakataren MDD Antonio Gutierres.
Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattabawa hanu a jeddaha a gaban khalifan wuraren ibada masu tsarki, abune da zai shiga cikin tarihi kuma zai kawo gagarumin cigaba ga mutane Ethiopia da Erirea, kuma zai taimaka wajen karfafa tsaro da daidaito a fadin yankin baki daya.
Eritrea, wacce ada lardi ne a kasar Habasha, ta balle ne a shekarar 1993. Rikicin da ya haddasa yaki na tsawon shekaru 2, tare da halaka kimanin mutane dubu dari bakwai. Daga bisani zaman doya da manja ya biyo baya.

en_USEnglish
en_USEnglish