AMBALIYAR RUWA DA AKA SAMU A JIHOHIN NAJERIYA DALILIN WATA ANNOBA DA TA KAI MATSAYIN ANNOBAR KASA GABA DAYA NE

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyana cewa ambaliyar ruwa da aka samu a jihohin Kogi da Anambara da Delta da Neja a matsayin wata annoba da ta kai matsayin annobar kasa gaba daya ba wai jihohin ba kadai.

Direkta-Janar na hukumar Mustapha Maihaja ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai wata ziyarar gani da ido a gabar kogin Neja dake garin Lokoja a jiya Litinin, inda yake zagayen ziyarar jihohin da hukumar ta sanya su cikin jerin jihohin da za a kula da batun ambaliya.

Yace dalilan da yasa hukumar take wannan zagaye, shine jajantawa al’ummar da ambaliyar ruwan ta shafa, wanda da yawansu suka rasa muhallinsu da gonaki masu yawan gaske.

Ya kuma kara da cewa zasuyi kokari wajen dakile faruwar hakan anan gaba. Ya ce hukumar su da gwamnatin jihar Kogi suna kokarin ganin sun shawo kan wannan al’ammarin, tare da taimakawa wayanda alamarin ya shafa.

en_USEnglish
en_USEnglish