AN AMINCE DA NADIN DR NASIRU YUSUF GAWUNA A MATSAYIN SABON MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KANO

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da nadin kwamishinan gona, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kano.
Da yake karanta jawabin amincewar shugaban majalisar Kabiru Alhassan Rurum, ya ce majalisar ta gamsu da cancantar Nasiru Yusuf Gawuna, biyo bayan tantance shi da kuma tambayoyi da ya amsawa yan majalisar a yau.
Bayan tantancewar da kuma takaitacen zaman sirri da ‘yan majalisar suka gudanar, shugaban majalisar Kabiru Alhassan Rurum, ya karanta matsayin da majalisar ta cimma na amincewa da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin mataimakin gwamna daga yau.

Da yake mayar da martini kwamshinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya ce batun mukamin da sabon mataimakin gwamnan yake rike da shin a kwamishinan harkokin gona harma da mukamin kwamishinan ilimi da tsohon gwamna Farfesa Hafiz Abubakar ya rike, har yanzu gwamnati ba ta fidda matsaya kan cewa ko sabon mataimakin gwamnan zai hada dukannin mukaman ko akasin haka.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki, ya rawaito cewa, nadin sabon mataimakin gwamnan ya biyo bayan ajiye aiki da mataimakin tsohon gwamnan ya yi tun tsahon watanni da suka gabata.

en_USEnglish
en_USEnglish