GWAMNATIN JIHAR KANO TA TABBATAR DA MUTUWAR MUTANE 31 TARE DA RUSHEWAR FIYE DA GIDAJE 10,000

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum 31 tare da rushewar fiye da gidaje 10,000 sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a kananan hukumomi 15.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jiha wato SERERA Malam Ali Bashir,ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Litinnin,yana mai cewa an kiyasta nera biliyan biyar a matsayin dukiyar da aka yi asarar sanadiyyar ambaliyyar.
Ya kuma kara da cewa, manoma fiye da 35,000 ne ambaliyar ta shafa a kananan hukumomi 8 na jihar kano wanda suka hada da wudil da Warawa da Gabasawa da kuma garin Gaya.
Malam Bashir ya kuma bayyana cewa, ambaliyar ta mamaye gonaki da dama ain da ya yi sana diyyar asarar amfanin gonar.
Haka zalika hukumar ta tabbatar da karbar bayanai daga kananan hukumomi 8 da ambaliyar ta shafa, za kuma ta mikawa gwamnatin jiha cikakken rahoton bayanin da nufin daukar matakin da ya dace.

en_USEnglish
en_USEnglish