GWAMNATIN JIHAR KANO ZATA KASHE NAIRA MILIYAN SITTIN WAJEN CIYARDA DALIBAN MAKARANTUN KWANA

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta kashe sama da naira miliyan sittin wajan ciyarda daliban makarantun kwana a bana.
Shugaban hukumar kula da manyan makarantun sakandire, Dr Hussain Umar Ganduje ne ya bayyana hakan, ta bakin jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Yushe’u Hamza Kafin ciri, yayin da hukumar ta ke sabun ta bada kwangilar kayan abincin ga ‘yan kwangilar.
Ya ce za su bibiyi yadda za a ciyar da daliban tare da sa idanu don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ya kuma ce, sun ware makarantun jeka ka dawo guda shida don tantance dalivan da suka fara halartar makarantun bana don yi musu kyauta ta musamman.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, Walida Nura daga makarantar ‘yan mata ta Hotoro ita ce dalibar da ta fara zuwa makaranta a bana.

en_USEnglish
en_USEnglish