SHUGABAN KASAR NAJERIYA YA SAUKA A JIHAR OSUN A YAU TALATA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka birnin Osogbo dake jihar Osun a yau Talata don halartar taron gangamin kamfen din yakin neman zaben dan tankarar gwamnan jihar Osun a jami’iyar APC, Gboyega Oyetola da za yi a ranar asabar.
Cikin tawagar akwai, uban jam’iyar Ahmad Bola Tinubu da shugaban jam’iyar APC, Adams Oshiomole da kuma sauran gwamnonin jam’iyar APC ciki harda gwamnan jihar Osun mai baring ado Ra’uf Aregbisola da gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, kuma babban daraktan yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Osun a jam’iyar APC.
Sauran tawagar, sun hada da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I da da sauran jigajigan jam’iyar APC.

en_USEnglish
en_USEnglish