YARA KANANA MILYAN 6 DA DUBU 300 SUN MUTU SAKAMAKON KAMUWA DA CUTUTUKA

Hukumar lafiya da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, sun bayyana cewa yara kanana milyan 6 da dubu 300 ne suka mutu a cikin shekarar da ta gabata sakamakon kamuwa da cututukan da ake iya daukar matakan kauce musu, abin da ke nuni da cewa yaro daya ne ke mutuwa a cikin kowacce dakika biyar.
Rahoton ya bayyana cewa yara milyan 5 da dubu 400 na wannan adadi sun mutu ne suna da shekarun da ba su wuce biyar ba a duniya, tare da gargadin cewa matukar dai ba a dauki matakan da suka dace ba, yawan wadanda za su mutu zai kai milyan 56 kafin shekara ta 2030.
Daraktar sashen tara alkaluma a hukumar UNICEF Laurence Chandy, ta ce tabbas an samu gagarumin ci gaba a kokarin rage rsasuwar yara kanana a duniya tun cikin shekarar 1990, amma duk da haka wasu milyoyi na ci gaba da mutuwa sakamakon matsalolin da za a iya kauce musu.
Laurence ta kara da cewa, karancin magunguna da rashin ruwa mai tsafta da rashin wutar lantarki su ne manyan matsalolin da suka haddasa rasuwar rabin yara ‘yan kasa da shekaru 5 musamman a kasashen Afrika da ke Kudu da Sahara, sai kashi 30 a yankin Kudancin Asiya.

en_USEnglish
en_USEnglish