AN SAKO MALAMAI UKU NA KWALEJIN LAFIYA DAKE JIHAR KADUNA

A daren jiya talata ne aka sako Malamai uku na Kwalejin Lafiya ta Shehu Idris dake Makarfi a jihar kaduna, bayan yini biyu da suka shafe a hannun masu garkuwa da mutane.
Shugaban Kwalejin Yusuf Yakubu ne, ya tabbatar da dawowar wadannan malamai. Da misalign karfe 8:00 na daren jiya.
Ya ce sai da suka cimma matsaya da masu garkuwar kafin aka sako malaman.
Tunda fari dai Masu garkuwa da mutanen sun sace malaman Kwalejin uku ne a ranar lahadin da ta gabata, yayin da suke kan hanyarsu ta tafiya Makarfi daga garin Zariya.

en_USEnglish
en_USEnglish