AN YI KIRA GA GWAMNATIN TARAYYA DA TA TABBATAR DA SABON TSARIN KARIN ALBASHI GA MA’AIKATAN GWAMNATI

Kungiyar bunkasa ilimi da cigaban Demokradiyya wato SEDSAC, tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da sabon tsarin karin albashi ga ma’aikatan gwamnati.
wannan kiran ya fito ne ta bakin babban Daraktan kungiyar Kwamared Hamisu Kofar Na’isa, yayin ganawar sa da gidan rediyon dala.
Ya ce karin albashin abu ne da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin ma’aikatan kasar nan.

Ya kuma kara da cewar, kamata yayi bankuna su rinka biyan kananan kudi duba da cewa wasu daga cikin mutane daga banki suke wucewa kasuwa.

Kwamared Hamisu Kofar Na’isa ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da su rinka sassautawa al’umma acikin kasuwancin su duba da yadda ake cikin matsin rayuwa.

en_USEnglish
en_USEnglish