MAJALISAR ZARTAWAR KASAR INDIYA TA HARAMTA YI WA MATA SAKI UKU LOKACI DAYA

Majalisar zartarwar kasar Indiya ta amince da doka mai tsauri da ta haramta yi wa mata saki uku lokaci guda.
Ministan doka na kasar Ravi Shankar Prasad ya ce daga yanzu za a rika hukunta duk mutumin da ya yi wa matarsa saki uku lokaci guda.
Yin saki uku lokaci guda ya zama tamkar ruwan dare a tsakanin maza Musulmi.
A cewar ministan, majalisar zartarwar ta amince da dokar ne saboda maza na ci gaba da aiwatar da irin wannan saki duk kuwa da hukuncin da kolin kolin kasar ta zartar na haramta shi.
Gwamnatin India ta dade tana kokarin ganin majalisar dokokin kasar ta amince da hukuncin daurin shekara uku ga duk mutumin da ya keta wannan doka.
Sai dai ‘yan hamayya na so a yiwa dokar gyaran fuska ta yadda ba za a yi amfani da ita wajen musgunawa jama’a ba.

en_USEnglish
en_USEnglish