WANI LAUYA A NAN KANO YAJA HANKALIN MA`AURATA DASU RINKA KYAUTATA ZAMANTAKEWARSU A ZAMAN AUREN SU

Wani lauya mai zaman kansa a nan kano barrister Umar Usman Danbaito, ya bayyana cewa, rashin daukar matakin kotu da wasu mataye kanyi idan sun samu sabani da mazajensu, shi ne abun dake haddasa matsalolin mata masu hallaka mazajensu.
Barrister Danbaito ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin shari’a a aikace na nan gidan rediyon Dala fm da safiyar yau Laraba.
Ya ce, idan miji yana cin mutuncin matar sa to kamata yayi ta kai karar sa kotu domin neman hakkin ta, maimakon ta dauki matakin barbada masa shinkafar Bera ko kuma amfani da makami domin kashe shi.
TRACK UP
Barista Umar Usman Danbaito ya kuma ja hankalin mazaje da su ji tsoron A…. su kyautatawa iyalan su domin samun zaman lafiya mai daurewa.

en_USEnglish
en_USEnglish