AN CI GABA DA CIN KOFIN MA’AIKATAN JAMI’O’IN KASAR NAN DAKW WAKANA A JAMI’AR ILORI TA JIHAR KWARA

An cigaba da gasar cin kofin ma’aikatan jami’o’in kasar nan dake wakana a jami’ar Ilori ta jihar Kwara karo na 13.
A wasan kwallon hannu jami’ar Wudil ta yi rashin nasara a hannun jami’ar Lafia da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da na karshe.
A wasan kwallon kafa kuwa jami’ar Wudil na da 3 jami’ar tarayya ta Oyo na da 1 wanda ya baiwa jami’ar Wudil damar zuwa wasan daf da na kusa da na karshe.
A wasan kwallon hannu kuwa jami’ar Wudil ta doke jami’ar Afebabalola da ci 2-0.
A wasan kwallon Badminton kuwa na ‘yan wasa bibiyu jami’ar Wudil na da 1 jami’ar Bayero na da 2.
A wasan Draft na turawa kuwa jami’ar Wudil ta sami nasara da ci 2-0a hannun jami’ar jiha ta Ekiti, haka zalika jami’ar ta Wudil ta kuma samun nasara da ci 2 da nema a hannun jami’ar Namdi Azikwe.
Sannan jami’ar ta Wudil ta doke Benin a wasan na Draught da ci 2-0.

en_USEnglish
en_USEnglish