AN SHAWARCI HUKUMOMI A NAN JIHAR KANO DA SU SANYA ‘YA ‘YAN SU A MAKARANTUN GWNATI

Wani mai rajin cigaban Ilimi anan Jihar Kano Kwamared Auwal Rabiu Babban wando, ya shawarci hukumomi da su sanya ‘ya’yan su a makarantun gwamnati.
Kwamared babban wando ya bayyana hakan ne ya yin ganawar sa da gidan rediyon Dala.
Ya ce kamata yayi gwamanti tayi doka cewar, dukkan ‘ya’yan ‘yan majalisu da gwamnoni da kuma ‘ya’yan Talakawa su kasance a makarantu daya.

Ya kuma kara da cewa malaman makarantu su ji tsoron A… su koyar da dalibai yadda ya kamata.

Kwamared Auwal Rabiu Babban wando ya kuma ja hankalin al’umma musamman matasa da su sanya harkokin Ilimi a gaba, bawai su zauna kawai ko kuma su shiga bangar siyasa ba.

en_USEnglish
en_USEnglish