AN YI KIRA GA MASU KARA DA RANAR ZUWAN SU KOTU TA SHIGA RANAKUN YAJIN AIKI

Kakakin babbar kotun jihar Kano baba Jibo Ibrahim ya yi kira ga masu kara da ranar zuwan su kotu ta shiga ranakun da ake yajin aiki, da su halacci kotun da zarar an gama yajin aikin dan sauya musu wata ranar.
Baba jibon ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan kammala shirin shari’ah a aikace na nan Dala fm a yau.
Yace da yawa mutane idan an sami irin wannan matsalar su kan kauracewa kotunan gaba daya.
Track up
Ya kuma ce akwai matsala ga wadan da suka ki halartar kotun bayan an kammala ko an jin gine yajin aikin.

en_USEnglish
en_USEnglish