YAU AKE SAKE WANI BANGARE NA ZABE A JIHAR OSUN

Daga can jihar Osun kuwa a yau ne za’a sake wani bangare na zaben gwamnan jihar.
A zantawar manema labarai da Shugaban hukumar zabe ta INEC a jihar, Segun Agbaje, Ya ce za a fara kada kuri’u ne daga karfe takwas na safe zuwa karfe biyu na rana, kuma wadanda suke kan layi zuwa karfe biyu za’a ba su damar kada kuri’a.
Ya kuma kara da cewa hukumar a shirye ta hukunta duk wanda aka samu da sabawa doka a yayin da ake karasa zaben.

en_USEnglish
en_USEnglish