AL’UMMAR UNGUWAR KADAWA SUN CE BA ZA SU KARA ZABAR SUK WANI DAN SIYASAR DA YAKI CIKA MUSU ALKAWURAN SU BA

Al’ummar unguwar Kadawa dake yankin karamar hukumar Gwale a nan Kano, sun ce ba za su kara zabar duk wani dan siyasar da yaki cika masu alkawuran su ba a zabukan 2019 mai zuwa.
Shugaban kungiyar ci gaban unguwar Kadawa wato Kadawa Community Development, Alhaji Babangida Adamu, ya ce, yankin na su na fama da tarin matsaloli, kuma sun bi duk hanyar da suke ganin za’a samu mafita amma abin ya ci tura.
ya ce a duk sanda siyasa ta gabato sukan yi alkawarin biya masu bukatun su ta hanyar yi masu aiki amma dazarar sun dare kan mulki sai su nemesu su rasa.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana irin tarin matsalolin da suke fuskanta.

Wakilin mu Auwal Hassan Fagge ya rawaito cewar, al’umma yankin na fatan masu ruwa da tsaki kan lamarin za su kawo musu daukin gaggawa, duba da tarin matsalolin da suke fuskanta na karancin ababen more rayuwa.

en_USEnglish
en_USEnglish