AN SOKE ZABAN DA AKA FARA YI A JIHAR ZAMFARA SAKAMAKON ZARGIN TABARBAREWAR TSARO A LOKACIN ZABEN

kwamitin zaben fitar da gwani na masu neman takarar gwamna a jam`iyyar APC ya soke zaben da aka fara a jihar Zamfara sakamakon zargin tafka magudi da tabarbarewar tsaro a lokacin zaben.
A jiya ne dai aka fara zaben bayan an yi ta turka-turkar kusan mako guda kafin fara zaben, sai dai gwamnatin jihar ta ce zaben bai soku ba, kuma za ta ci gaba da gudanar da shi.
Ita kuwa uwar jam’iyyar APC ta kasa ta aike wa manema labarai wata sanarwa tana mai cewa an soko zaben, kuma za a sanya wata ranar ta daban domin gudanar da shi.
Kwamitin zaben, wanda ya yi jawabi ga `yan jarida a hedikwatar `yan sandan jihar Zamfara, ya yi zargin cewa akwai matsaloli da dama wadanda suka jibanci magudi da tsaro da suka dabaibaye zaben, kuma babu abin da ya fi dacewa face soke shi.
Shugaban kwamitin zaben Dr Abubakar Fari, ya yi zargin cewa akwai wasu ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan zabe da suka karbe takardun zabe suka kuma cike sakamakon da suke so a sanar da mutane.

en_USEnglish
en_USEnglish