AN KASA SAMUN SAHIHIN SAKAMAKON ZABEN FIDDA GWANIN ‘YAN TAKARKARUN MAJALISUN DOKOKIN JIHA DA NA TARAYYA A NAN KANO

Har yanzu ankasa samun sahihin sakamakon zaben fidda gwanin ‘yan takarkarun majalisun dokokin jiha dana tarayya na jam’iyyar APC a nan Kano.
Zaben wanda aka gudanar ajiya ya zo da rudani sakamakon yadda bangaren kowane dan takara ya ke fidda sanarwar cewa gwaninsu ne ya lashe zaben.
A bangaren majalisar Wakilai ta tarayya a mazabar karamar hukumar birni, anjiyo yadda a karon farko sanarwa ta fita cewar, Sha’aban Ibrahim Sharada ya kada abokan karawar sa Uku, yayin da daga bisani kuma sai wata ta sake fita cewa, Muntari Ishak Yakasai ne ya lashe zaben, inda ya doke a bokan karawar Uku ciki har da Sha’aban din.
Wannan ta sanya Muntari Ishak din bayyana murnar sa ta lashe zaben.

Daga bisani dai rahotanni sun sake nuni da cewa, tun da farko ma, shi Sha’aban din anyi masalaha ne, inda sauran ‘yan takarkarun suka janye masa.
Makamancin irin wannan al’amari dai, shi ne har yanzu ke cigaba da faruwa a tsakanin masu neman Jam’iyyar ta APC ta sahhale musu takara a matakin majalisar dokoki da kuma ta wakilai a tarayya.

Rudanin dai ya samo asali ne sakamakon rashin ayyana wanda keda alhakin sanar da sakamakon zabubbukan tun kafin a gudanar da shi a jiyan.

en_USEnglish
en_USEnglish