AN YI KIRA GA AL’UMMA DA SU DUBA MUTUMIN DA ZA SU ZABA A LOKACIN ZABE MAI ZUWA NA 2019

Kungiyar nan mai rajin bunkasa Ilimi da cigaban Demokradiyya wato SEDSAC, tayi kira ga al’umma da su duba mutumin da za su zaba, a lokacin babban zabe mai zuwa na 2019.
Shugaban kungiyar Kwamred Umar Hamisu Kofar Na’isa ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala fm.
Umar Hamisu Kofar Na’isa ya ce, duba da irin abubuwan da su faruwa ayanzu a kwai bukatar al’umma suyi karatun ta nutsu akan wadanda zasu zaba.

Ya kuma kara da cewar, ya zama wajibi shugabannin da za a zaba, su kasance masu kyautatawa al’ummar su.

Kwamared Umar Hamisu Kofar Na’isa, ya kuma yi kira ga matasa da su guji shiga bangar siyasa, musamman a wannan lokaci na zabe.

en_USEnglish
en_USEnglish