BABBAN LIMAMIN MASALLACIN USMAN BIN AFFAN YA BUKACI DA A WARE WASU MALAMAI NA MUSAMMAN MASU AMSA FATAWAR AL’UMMA A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA

Babban Limamin masallacin Usman Bin Affan da ke Gadon kaya, Mallam Abdallah Usman Gadon kaya, ya bukaci da a ware wasu malamai na musamman wadanda zasu ringa amsa fatawar al’umma a shafukan sada zumunta na intanet.
Mallam Abdallah Gadon Kaya ya yi wannan kiran ne, Jim kadan bayan kammala shirin Rayuwa Abar koyi na nan gidan rediyon Dala da safiyar yau juma’a.
Ya ce, duba da yadda ake samun yawaitar bude shafukan sada zumunta da sunan malamai, kuma masu budewar suci gaba da bada fatawa dai da son ransu.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta rinka bada kulawa ta musamman ga irin wadannan malaman masu bada fatawar.

Mallam Abdallah Gadon Kaya ya kuma ja hankalin malaman, da su ji tsoron A… a cikin fatawowin da za su bayar domin samun ingantacciyar al’umma.

en_USEnglish
en_USEnglish