JAM’IYYAR APC ZA TAYI WANI KWAMITI NA MUSAMMAN DA ZAIYI DUBA AKAN ZABUKAN FIDDA GWANI NA GWAMNONI A WASU JIHOHIN KASAR NAN

Jam’iyyar APC za tayi wani kwamiti na musamman da zaiyi duba akan zabukan fidda gwani na Gwamnoni a jihar Imo da kuma Jihar Zamfara.
Shugaban Jam’iyyar na Kasa Kwamred Adams Oshiomole ne ya tabbatar da hakan yau juma’a a shelkwatar Jam’iyyar ta Abuja.
Adam Oshiomhole ya ce, sabon kwamitin zaiyi duba na tsanaki akan dukkan zabukan da aka gudanar a Jihohin biyu, ya kuma kawo rahoton sa.
Jihohin biyu dai sun samu matsaloli a yayin gudanar da zabukan na sun a cikin gida.

en_USEnglish
en_USEnglish