JAM’IYYAR PDP TA GUDANAR DA WATA ZANGA ZANGA DANGANE DA RASHIN AMINCEWAR SU DA SAKAMAKON ZABEN OSUN

Comments are closed

Jam’iyyar PDP ta gudanar da wata kwarya-kwaryar zanga zanga don nuna kin amincewarsu da sakamakon zaben da aka gudanar kashi na biyu a zaben gwamnan jihar Osun, wanda hukumar zabe ta bayyana, jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben.
Zanga zangar da jam’iyar ta gudanar a yau karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar, ta kasa Uche Secondus ya samu halartar masu neman jam’iyyar ta tsayar dasu takarar shugaban kasa a zaben da za a gudanar a shekarar 2019.
‘Yan takarar sun hada da shugaban majalisar dattijawa Abubakar Bukola Saraki, da gwamman jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da sauransu.
Masu zanga-zangar wanda suka hau motar kanta ta diban kaya, sun bukaci hukumar zabe ta kasa INEC ta tsame kanta a cikin shiga harkokin gwamnati mai ci tare da gudanar da gaskiya a cikin zabuka.

Comments are closed.