AN BUKACE AL’UMMA DA SU RINKA TALLAFAWA GIDAJEN MASU RANGWANIN HANKALI

Mai kula da gidan masu rangwamin hankali na Dorayi dake karamar hukumar Gwale, Aminu Garba Suleman, ya bukaci al’umma da su rinka tallafawa irin wadannan gidajen na masu fama da lalurar ta tabin kwakwalwa da kayayyaki musamman ma a lokutan sanyi da yake karatowa.
Aminu Garba, ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala, a wani bangare na bikin ranar kulawa da masu lalurar kwakwalwa da ya gudana a jiya.
ya ce baya ga taimako da gwamnati ke baiwa gidajen akwai bukatar su ma al’umma su rinka tallafawa masu lalurar ta kwakwalwa.

Aminu Garba Suleman ya kuma bukaci gwamnati da ta cigaba da tallafawa gidajen masu lalurar ta tabin kwakwalwa musamman ma magunguna da kuma kayan sawa.

en_USEnglish
en_USEnglish