RASHIN SANIN DOKA BA HUJJA BA NE DUBA DA YADDA MUTANE SUKE AIWATAR DA AL’AMURA BA TARE DA YIN AIKI DA DOKA BA

Kakakin babbar kotun jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya bayyana cewa rashin sanin doka ga kowane dan kasa ba hujja ba ne duba da yadda mutane suke aiwatar da al’amura ba tare da yin aiki da doka ba.
Baba Jibo Ibrahim, ya bayyana hakan ne bayan kammala shirin shari’a aikace na nan gidan rediyon Dala.
Ya ce aiki da doka ya na farawane tun daga cikin gida wanda kuma ya yi aiki da dokar yakan zauna lafiya.

A wani bangaren kuma, ya ce a sauye-sauyen da aka samu ga alkalan manyan kotunan jiha, duk wata shari’a dake gaban kotunan da lamarin ya shafa za a sauya masu kotuna don cigaba da sauraran karar.

Baba Jibo Ibrahim ya kara da cewar, suma wadanda suke tsare a gidajen yarin za a sanar da jami’an gidan yari sauyin kotunan da aka samu.

en_USEnglish
en_USEnglish