RUNDUNAR ‘YAN SANDAR JIHAR IMO TA SAMU NASARAR CETO SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR IHIALA DA AKA SACE

Rundunar ‘yan sandar jihar Imo ta samu nasarar ceto shugaban karamar hukumar Ihiala dake jihar Anambra, mai suna Ifeanyi Odimegwu, da dansa Tochi Odimegwu da kuma direbansa Boniface Uche wadanda suka yi garkuwa da su.
Kwamishinan ‘yan sandar jihar Imo Dasuki Galadanchi ne ya bayyana hakan a garin Owerri, inda ya ce, an sace shugaban karamar hukumar ne a kan babban hanyar Owerri ranar Lahadi da safe.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa, lokacin da masu garkuwan suka ga jami’an ‘yan sanda a cikin dajin Umuapu, inda masu garkuwar suka yi sansani, sai suka gudu tare da wasu makudan kudade da kuma sauran kayayyakin su.
Ya kuma kara da cewa, shugaban karamar hukumar ya yi matukar kaduwa inda aka garzaya da shi zuwa asibiti.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, rundunar ‘yan sanda na gudanar da bincike akan wadanda ake zargi da laifin garkuwa da mutanen, inda da zarar sun kammala binciken za su gurfanar da su agaban kotu.

en_USEnglish
en_USEnglish