AN GARGADI AL’UMMA DA SU GUJI CIN ZARAFIN YARA MATA

Shugaban Kungiyar kare hakkin Dan’adam da Jin kai ta kasa, Alhaji Muhammad Bello Gadon Kaya, ya gargadi al’umma da su guji cin zarafin yara mata, musamman a wannan zamani da muke ciki.
Muhammad Bello Gadon kaya, ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala, a wani bangare na bikin yara mata na duniya da ya gudana a jiya.
Ya ce, kamata yayi masu halayyar cin zarafin yara mata su guji wannan dabi’ar tare da jin tsoron Allah a zukatan su.

Muhammad Bello Gadon kaya, ya kuma yi kira ga iyaye mata su sani cewa haki ne da ya rataya a wuyan sun a kula da ‘ya’yan da ya basu kuma zai tambaye su a ranar gobe kiyama.

en_USEnglish
en_USEnglish