BABBAN LIMANIN MASALLACIN MADINA, YA JA HANKALIN AL’UMMA DANGANE DA MATSALOLIN DA MUTUWAR AURE KE HAIFARWA

Babban limamin masallacin madina, Ali bn Abdulrahman Al-Huzaifi, ta cikin hudubar sallar juma’ar sa ta yau, ya ja hankalin al’ummar duniya dangane da matsalolin da mutuwar aure ke haifarwa.
Daga nan dakin mu na yada labarai, Malam Aminu Kidir ya bibiyi hudubar gamu kuma tare.

Daga nan jihar Kano ma dai wani bincike da hukumar Hizba ta gudanar ya nuna cewa, mata suna cikin matsananciyar damuwa sakamakon matsalolin zamantakewar Aure, kamar yadda mataimakiyar babbar kwamandar hukumar a bangaren Aure Malama Zahra’u Muhammad ta tabbatar.

Malama Zahra’u Muhammad, ta kuma bukaci ma’aurata da su rinka hakuri da juna tare da bin dokokin aure kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

en_USEnglish
en_USEnglish