BECHI UNITED ZA TA BARJE GUMI DA DAMBARE EMIRATE A WASAN KARSHE RANAR LAHADI

A ranar Lahadi ne Bechi United za ta barje gumi da Dambare Emirate a wasan karshe na cin kofin Kumbotso a filin wasa na GSS Kumbotso, a nan kuwa gamayyar kungiyoyin masu buga waya a kafafen yada labarai na jihar Kano zasu fafata a wasan sada zumunci da Freedom Rediyo da yammacin yau a filin wasa na cikin gidan rediyo Freedom.
A cigaba da wasan cancanta na shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika na shekarar 2019 da za’ayi a kasar Kamaru, wasan da aka buga a jiya, kasar Congo ta doke kasar Laberiya da ci 3 da 1.
Wakilin mu a fagen wasanni Abba Haruna Idris na da cigaban labarin da ma wasu labaran wasannin.

en_USEnglish
en_USEnglish